Sakon Osinbajo Zuwa Ga CBN Kan Crypto Currency A Nigeria

Mataimakin shugaban kasa Professor Yemi Osinbajo yana jaddada wa babban bankin Nigeria cewa kasuwancin kudi na Cryptocurrency guguwa ne mai karfi da ya tunkaro duniya wanda zai mamaye komai na harkan kudi da bankuna

 

Osibanjo yace Cryptocurrency zai zo ya kalubalanci harkokin bankuna da kudi da ake amfani dashi a yanzu,  Cryptocurrency zai mayar da su tsohon yayi, kuma ba da jimawa ba, don haka ya zama dole mu rungumeshi tun yanzu

 

Jama'a nan gaba kamfanoni da yawa zasu dena ciniki da kudi zasu koma na Cryptocurrency, manyan jami'o'i zasu koma karban coin da token a matsayin kudin makaranta

 

Mutanenmu har yanzu gani suke harkan Cryptocurrency kamar almara ne da kuma asara, ko ni kafin na tsunduma nayi irin wannan tunani da fargaba, amma da na fara neman ilminsa da zuba jari a ciki na fahimci yafi komai kawo alhari, Cryptocurrency ya wuce duk inda muke tunani

 

Matasan da sukayi nisa a wannan harkan yanzu sunfi karfin kowani irin aikin Gwamnati a Nigeria, sun mallaki gida mai kyau da motoci masu tsada,  suna daukar nauyin kansu da na iyaye da iyalansu, sun zama miloniyas a dalilin Crypto

 

'Yan uwa a tashi a nemi ilmin Cryptocurrency, ko ka mallaki digiri uku a ilmin kasuwanci baka san komai a Crypto ba, sai ka koya, Wallahi ko nawa mutum zai kashe ya koyi wannan harkar ba asara bane.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author