Shanyewar Ɓarin Jiki: Ko Daga Ina Matsalar Take? Karanta Kaji Dalili

Wannan cuta ta shanyewar ɓarin jiki da ake kira da "brain stroke" a turance, wanda aka fi sani da ciwon faralayis (paralysis) na faruwa ne sakamakon katsewar jinin da ke kai wa ƙwaƙwalwa iskar oksijin da sinadarin gulukos, hakan na faruwa idan jijiyar jini a ƙwaƙwalwa ta fashe ko kuma ta toshe.
 
Hukumar lafiya ta duniya ta ayyana cewa a kowace shekara mutum miliyan 15 ne ke samun wannan cuta, kuma daga cikinsu mutum miliyan biyar ne ke mutuwa nan take ko bayan wani lokaci sakamakon cutar, wata miliyan biyar ɗin kuma su rayu amma su ƙare rayuwarsu da sauran nakasu a sassan jikinsu, sannan ragowar miliyan biyar ɗin ƙarshe su warke sumul kamar ba su yi cutar ba.
 

Mutanen da ke da haɗarin kamuwa da wannan cuta sun haɗa da:

1) Masu hawan jini,
2) Masu ciwon siga,
3) Mashaya taba-sigari,
4) Masu ciwon sikila (amosanin jini),
5) Masu tararren kitse a cikin jini,
6) Masu ƙiba ko teɓa,
7) Mashay giya / barasa,
8) Masu ciwon zuciya,
9) Masu ɗabi'ar ƙin motsa jiki,
10) Masu shekaru fiye da 30, da dai sauransu.
Alamun da ke gargaɗin kamuwa da wannan cuta sun hada da:
1) matsananci ciwon kai,
2) hajijiya / juwa,
3) nauyi ko sagewar ɓarin jiki
4) karkacewar baki / fuska musamman ga masu hawan jini ko ciwon siga,
5) Fitar hankali tare da faɗuwa kwatsam.
Alamun kamuwa da shanyewar ɓarin jiki sun haɗa da:
1) shanyewar ko raunin ɓarin jiki, hagu ko dama, wani lokacin duka biyun,
2) fitar hankali ko suma,
3) amai,
4) ɗaukewar, nauyi ko sarƙewar magana,
5) karkacewar baki, da sauransu.
 
Ga waɗanda hankalinsu bai fita ba a lokacin afkuwar wannan cuta su kan bayar da rahoton matsanancin ciwon kai dab da faruwar abin, gani dishi-dishi ko garara-garara, da dai sauransu.
 
Wannan cuta tana zuwa ne kamar mutuwa, ana tafe, ana zaune, ana aiki, ana farke ko ana bacci. A duk lokacin da wani ya samu wannan cuta ana matuƙar buƙatar garzayawa da shi asibiti a cikin awanni uku da faruwar matsalar, saboda yawan jinkirin da aka yi a gida ko asibitin da babu ƙwararrun likitoci, to yawan jinkirin da za a samu kenan wajen warkewa.
 

A nan, muna sake jaddada kira ga al'umma kamar haka:

1) Musamman ga duk wanda ya san yana da hawan jini ko ciwon siga da su ɗinga zuwa asibiti ana sake duba lafiyarsu akai-akai ko da ba su jin wata matsala a jikinsu. Ba ma ga masu wannan matsaloli kawai ba, har ma ga masu lafiya.
2) Shan magungunan ciwon kai barkatai musamman ga wadanda shekarunsu suka miƙa ya zama ruwan dare a cikin al'umma, don haka, ga duk wanda ya sha maganin ciwon kai fiye da kwanaki uku jiwon bai daina ba, to lallai ne ya je asibiti domin ganin likita.
3) Har yanzu akwai masu ganin cewa wannan cuta bugun aljan ce hakan tatsuniya ce kuma ya saɓa wa bincike da likitancin zamani saboda haka a garzaya da mai irin wannan jinya asibitin da ya kamata.
4) Ga masu zaman jinyar masu wannan cuta, akwai buƙatar ƙara ƙoƙari da haƙuri, domin wasu daga cikin masu wannan cuta ba za su iya riƙe fitsari ko bahaya ba, kuma ba za su iya magana a gane ba, ba za su iya zama ko tashi ba. Komai sai anyi musu, sun dawo tamkar jarirai. Don haka, wannan cuta jarrabawa ce ba ga mai cutar kawai ba har ma ga dukkan iyalansa.
 
Daga ƙarshe, ga duk wanda ko wani ya samu wannan cuta, yana asibiti ne ko yana gida, sannan ka fahimci cewa daga cikin likitocin da suke duba shi babu likitocin fisiyo (Physiotherapists) to lallai aƙwai buƙatar ya tattauna da likitan kan gayyato likitocin fisiyo domin ci gaba da duba shi kafin matsalolin nakasa su fara bayyana a hannu ko ƙafa.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author