Shekarar 2023: Dole Mulki Ya Koma Kudu - Fashola

 
A ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, 2020, Ministan ayyuka da gidajen Najeriya, Babatunde Raji Fashola, ya yi magana game da siyasar 2023 a gidan APC, Raji Fashola SAN ya ce yadda tsarin kama-kama ya yi aiki a zaben 2015, ya kamata idan an zo 2023, a bar mulki ya koma wa ya yankin kudu.
 
An ruwaito cewa Fashola ya yi wannan magana ne a lokacin da wasu ‘ya ‘yan APC suke kokarin ganin an bar 'yan Arewa su cigaba da mulki, Ministan da yake tattauna wa da ‘yan jarida a Abuja, ya roki shugabannin jam’iyyarsu su bi tsarin da aka dauko wajen zaben yankin da zai yi takara a 2015.
 
Fashola ya ce ya kamata a bi tsarin da ake tafiya a kai ko da ba a rubuta alkawarin a matsayin yarjejeniya ba, ya ce da an yi hakan, to da magana ta kare, Amma ka da a karya alkawarin da ‘yan uwa su ka yi, dole a cika alkawarin nan.” Inji Fashola.
 
A cewar Raji Fashola, ‘ya ‘yan jam’iyya za su iya cewa yanzu ‘dan autan cikinsu ko mace ce za ta rike wata kujera, ya ce ko ba a rubuta ba, hakan ta zauna, Mai magana da yawun jam’iyyar APC mai mulki, Yekini Nabena ya shaida wa Punch cewa kafin zaben 2015, an tsara yadda za a yi takarar shugaban kasa.
 
Yekini Nabena yace shugabannin APC sun yarda a tsakaninsu cewa idan ‘dan Arewa ya gama mulki, za a mika tikiti ne zuwa yankin kudancin Najeriya, Da alamu rikicin da ake fama da shi a jam’iyyar APC mai mulki shi ne inda za a kai tikiti a 2023.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author