A ranar 10 ga watan Janairun 2011, ‘yan wasan kungiyar Barcelona suka zama na kan gaba a jerin wadanda zasu lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya wato Ballon d’Or.
Inda dan wasa Lionel Messi ya zama zakara a shekarar ta 2011, yayin da kuma takwaransa Davi Hernandez dan kasar Sipaniya ya zama na biyu, sai kuma daya dan uwan nasu wato, Andres Iniesta wanda shima dan Sipaniya din ne ya zama na uku a shekarar ta 2011.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona a lokacin tana kan ganiyarta na lashe wasanni da kuma manya-manyan kofuna domin watanni shida tsakani ta lashe kofin zakarun turai na Champions League kuma na hudu a tarihin kungiyar.
A yayin shekarar ta 2011, Messi da Davi da kuma Iniesta ne suka mamaye kyautar Ballon d’Or ta gwarzon dan kwallon duniya kuma Messi ne ya fara lashe kyautar Ballon d’Or din a shekarar ta 2009 da ta 2010 da ta 2011 da ta 2012 da kuma ta 2015.
A Ranar Asabar ne Barcelona ta je ta caskara Granada da ci 4-0 a wasan mako na 18 dan wasa Griezmann dai ya zura kwallaye biyu a raga rigis sannan kuma kaftin din kungiyar wato L.Messi shima ya zura kwallaye biyu a yayin karawar.
You must be logged in to post a comment.