Shugaba Buhari Ya Damu Da Harin Da Boko Haram Ta Kai A Kwapree Dake Jihar Adamawa

Shugaba Muhammadu Buhari, ya aikewa Al'umar garin Kwapree dake jihar Adamawa saƙon ta’aziyya kan mummunan harin da Boko Haram ta kai musu.
 
Sakon na shugaban ƙasar ya isa ne ta bakin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha inda bayyana cewar Shugaba Buhati na miƙawa jama’ar garin dake ƙaramar hukumar Hong sakon jaje.
 
Yace gwamnati zata ɗauki matakin magance matsalar da kuma taimakawa jama’ar garin sake gina garin nasu.
 
Yace ya shaida cewa an lalata gidaje sama da 78 da kuma shaguna 12.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author