Shugaba Buhari ya sauke manyan hafsoshin sojin Najeriya

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya fitar da takardar sauke manyan hafsoshin tsaron ƙasar  da kuma yi masu ritaya.

Takardar sanarwar da mai bawa shugaban kasa shawara kan kafafen watsa labarai Mr. Femi Adeshina ya sanaar tace shugaba Buhari ya amince da yiwa  manyan hafsoshin sojin ritayar.

Manyan hafsoshin sojojin sun ƙunshi babban hafsan tsaron na ƙasar Janar Abayomi Olonisakin da kuma babban hafsan sojin ƙasa Janar Tukur Buratai da babban hafsan sojin sojan ruwa Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas dana babban hafsan sojin sama Air Marshal Sadique Abubakar.

Shugaba Buhari ya kuma fitar da kuma naɗa sabbin manyan hafsoshin sojojin da za su maye gurbinsu kamar haka.

Janar Leo Irabor, shi ne wanda aka naɗa a matsayin babban hafsan tsaro; sai Janar I. Attahiru, shi kuma a matsayin babban hafsan sojan na ƙasar.

Da Rear Admiral A.Z Gambo, a matsayin babban hafsan sojin ruwa sai kuma Air-Vice Marshal I.O Amao, a matsayin babban hafsan sojan sama.

A cewar sanarwar, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya godewa manyan hafsoshin sojojin masu barin gado waɗanda yace "sun samu gagarumar nasara a ƙoƙarin da suke na samar da zaman lafiya a fadin ƙasar tare  ya kuma yi masu fatan alheri."

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author