Shugaban ƙaramar Hukumar Bauchi Yayi Alkawarin Shiga Cikin Shirin Fara Aurar Da Mata 200

Daga: Maimuna Ahmed Bauchi

Kungiyan dake fafutukan tara kudade domin shiga cikin rayuwar Talakawan jihar Bauchi kai tsaye ta fannoni masu yawa wanda zuwa yanzu ta tara miliyoyi kudade Domin shirin fara aurar da mata 200 cikin jihar Bauchi. Sun kai ziyara ma shugaban ƙaramar hukumar Bauchi Hon Mahmood Baba Maaji Abubakar. Yanda suka fayyace masa manufofin su tare da ayyukan da suka sanya a gaba a halin yanzu.
Jagoran kungiyar yan kwangila na jihar Bauchi Alh Kabiru Sani Sade wanda shirin ke karkashin kungiyar tasu shine yayi karin haske kan abubuwa da suka sanya a gaba a halin yanzu.
Jagoran shirin Domin talakawan jihar Bauchi
Abdulsamad Aminu shine ya karanto irin nasarorin da suka cimma na samu tallafin kudade masu tsoka a hannun al'umma.
Shugaban ƙaramar Bauchi Hon Mahmood Baba Maaji
Yace yayi na'am da Yunkurin nasu kuma yana tare da su kan wannan kyaukyawar manufa na Alheri dari-bisa-dari kuma da shi za'a insha Allah.
Ga masu sha'awan tallafa ma shirin suna iya kiran manajan shirin. Ta wannan Number
08099999796

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author