Suarez ya goge tarihin da Ronaldo ya kafa a gasar La Liga

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona daya sauya sheka zuwa kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid Luis Suarez, ya sha re tarihin da dan wasa Cristiano Ronaldo daya kafa na zura kwallaye 16 a cikin wasanni 17. 

A kakar wasa ta La Liga, abinda ya ba shi damar zama dan wasa mafi saurin jefawa abokan hamayya kwallo a raga, a yayin wasan da suka fafata tsakanin su da Celta Vigo ranar litinin.

Kungiyar kwallon kafa ta Celta Vigo ce ta fara zurawa Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid kwallo, sai dai masu masaukin baki sun sake zura kwallo inda aka tashi 2-2.

Sai dai abin baiwa Real Madrid da Barcelona dadi ba, ganin har yanzu akwai ragowar tazarar maki 8 maimakon maki 10 dake tsakaninsu.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author