Tabbas Duk Wanda Ya Saki Matarsa A Fim, Tamkar Ya Saki Matarsa Ta Gida Ne-Dr Sheik Ahmad Gumi

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Dakta Ahmed Gumi shi ma ya fitar da fatawar cewa duk dan wasan kwaikwayo da ya saki matarsa a cikin shirin fim to matansa na gida sun saku.
Manuniya ta ruwaito Dakta Ahmed ya amsa tambayar da wani yayi masa a yayin zaman karatun Fiqhu na mako-mako da yake yi a masallacin Sultan Bello zama na 57, ya ce ko shakka babu matansa na gida sun saku sai dai idan ya fayyace a yayin da yake yin sakin ko da a fim din ne.
Idan yana da mata sama da daya sai yace ya saki matarsa kuma bai fayyace wa yake nufi ba (misali yayi ishara ga wannan yar fim da ba matarsa bace) to duka matansa na gida sun saku inji Dakta Ahmed Gumi.
Wannan fatawa da batun saki a fim ya kuma zama da gaske na cigaba da tayar da ƙura a yankin Arewacin Najeriya, tun bayan da sanannen malamin mazaunin Birnin Kano Dr. Bashir Aliyu Umar ya bayar da fatawa akan wannan mas'alah.
An ruwaito jagororin Hausa Fim da dama ba su ji daɗin wannan magana ba, inda suke ganin tamkar an yi musu kutse cikin harkokin su wanda a fahimtar su wasan kwaikwayo ne.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author