Tausayin Talakawan Nijeriya Na Daga Cikin Sunnonin Shugaba Buhari, Cewar Ministan Hadi Sirika

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Ministan Harkokin Jiragen Sama, Alhaji Hadi Sirika ya bayyana cewa yana daga cikin sunnonin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, mutum ne mai tausayi al'umma kasar nan.
Hadi Sirika ya bayyana haka ne a karamar hukumar Batagarawa a lokacin da ya ke kaddamar da shirin nan, na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na samawa matasa dubu daya a kowacce karamar hukumar kasar nan, karkashin Ma'aikata samar da aikin yi ta kasa.
Ministan Harkokin Jiragen Sama, ya kara da cewa sakamakon tausayi ga talakkawa ke ciki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kirkiro shirye-shirye daban-daban duk da yawan al'umma, kuma an ce idan dambu ya yi yawa, bai jin mai. Kullum muka zauna majalisar zartaswa, da ya ke Shugabanta, ana kokarin a fiddo wasu tsare-tsaren da za su inganta rayuwar masu karamin karfi, domin dakushe radadin rashi ko talauci, duk da ba mai iyawa dan Adam sai Allah. Amma muna bakin kokarin mu kamar irin su Trader Money da N-power da kuma conditional cash transfer, wadanda suna tafiya ne kai tsaye ga talakkawa, domin su ji dumin gwamnati a jikin su.
Hadi Sirika ya ci gaba da cewa irin wannan salon mulki na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wato na gaba ya tausayawa na kasa da shi, idan Allah ya ba ka mulki ya kuma bada wuyan dauka, da addu'o'in abinda za ka yi, ya yi wa al'umma amfani. Insha Allah gwamnati tarayya za ta ci gaba da samar da sabbin dabaru, na dakushe tsanani da kaffin talauci.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author