Tirkashi: Sai Na Kashe Mutane Sannan Nake Samun Kudin Shan Giya Da Hutawa Da Budurwata – Mai Laifi

Wani matashin mutum mai kimanin shekaru 30 mai suna, Tajuddeen Monsuru ya yarda da laifin da ake tuhumarsa dashi na amfani da sassan gangar jikin dan Adam yanayin tsafi tare dakuma cin naman yana korawa da ruwan giya a duk lokacin da yake cikin nishaɗi.

Da yake amsa tambayoyin ga yan jarida a lokacin da hukumar yan sanda tayi ram dashi da wasu masu aikata manyan laifuka a hedkwatarsu dake garin Osogbo acikin jihar Osun, yace shi da budurwarsa ne da kuma wani mai suna Alan Mutiyat suke aikata hakan a duk lokacin da suka so.

“Sannan muna kashe mutane ne bayan sun yarda da mu, domin mafi yawan lokuta har bacci muke yi tare da su kafin cikin dare mu kashe su, sai muyi gunduwa-gunduwa da su don sayar da sassan jikin nasu.

“Bayan mun sayar sai kuma mu tafi gurin holewa da suke sayar da giya domin morewa rayuwarmu kuma muji dadi.

“A wani lokaci ma sai dana taba kashe budurwata da wani mutum aminina wanda abokina Akeem, ya kawo shi, Ni kuma bana jin komai bayan na gama aikata kashe su, ” a cewarsa.

Babban abokin harkar tasa mai suna Hamzat Akeem mai kimanin shekaru 25, ya amsa cewa shima ya kawo budurwarsa, Dafari gurin Monsuru nan take suka kashe ta aka bashi naira dubu ₦5,000 saboda rawar da ya taka na kawo budurwar tasa.

Shi kuma wani mutum mai suna Awayewasere Yusuf mai kimanin shekaru 37 yace sayi kan budurwar akan farashin naira dubu ₦20,000 domin yin tsafin samun kuɗi.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author