Tirkashi: Wani Direba Ya Gane Wanda Ya Taba Garkuwa Dashi A Cikin Fasinjojinsa A Sokoto

Wata takaddama ta faru a tashar mota ta garin Kwannawa dake karamar hukumar Dange-Shuni a jihar Sokoto, bayan da wani direba ya gane wanda ya taba garkuwa dashi a cikin fasinjojin dake motarsa.

Direban motar wanda aka sakaye sunansa, an yi garkuwa dashi ne a Kankara ta jihar Katsina, kusan watanni biyu da suka gabata.

Rahotanni sun nuna cewa, direban ya kai kusan sati uku a tsare a hannun masu garkuwan, bayan biyan makudan kudaden fansarsa wanda ba'a fadi adadin su ba.

Wanda ake ma zargin ya gamu da cikas ne, lokacin da ya shigo tashar motar domin tafiya kano, ba tare da yasan itace motar da suka yi garkuwa da direban ba.

Matukin Motar yayi saurin gane wanda suka yi garkuwar dashi ne, saboda abin bai dade da faruwa ba.

"Bayan fahimtar mai garkuwar, yayi gaggawar sanar da shugabannin kungiyar su, domin su sanar da jami'an hukumar 'yan sanda mafi kusa", wani dan kungiyar Direbobi na NURTW ya shaidawa manema labarai faruwar lamarin.

Shugabannin kungiyar NURTW sun canjawa direban motar da wani fasinja bayan da motar ta cika kuma ya nufi garin Shuni, An ruwaito cewa, anan ne jami'an hukumar 'yan sanda suka yi ram da wanda ake zargi domin kai shi ofishin su.

Da ake tuhumar wanda ake zargin, ya tabbatar da cewa shi dan kungiyar masu garkuwa da mutane ne kuma ana kiransa da suna " Hadari" tuni dai an hada shi da matukin motar domin amsa tambayoyi.

"Jami'an 'yan sanda sun matukar Mamaki ganin yadda matukin motar ya fadi sunan wanda ake zargin, duk da bayan lokacin da ake tuhumar", a cewar wakilin mu dake yankin.

An mayar da mai garkuwa da mutanen zuwa hedikwatar rundunar 'yan sanda dake garin Sokoto don zurfafa bincike.

Mai magana da yawun rundunar dake Sokoto, DSP Muhammad Sadiq ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya bayyana cewa suna nan suna bincike har yanzu.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author