August 13, 2020

Tuhume-Tuhume da ake Yiwa Shugaban EFCC Ibrahim Magu

Jerin Tuhume-Tuhume 10 Cikin 22 da ake Yiwa Ibrahim Magu.

  1. Tufka da warwara wajen lissafin kudaden da EFCC ta kwato hannun barayin gwamnati
  2. Ikirarin cewa N539bn aka kwato maimakon N504bn
  3. Rashin biyayya ga ofishin Antoni Janar na tarayya
  4. Rashin gabatar da isassun hujjoji domin dawo da Diezani Alison-Madueke Najeriya
  5. Bata lokaci wajen binciken kamfanin P&ID wanda ahakan ya kai ga rikicin da ake a Kotu anzu
  6. Kin bin umurnin kotu na sakin asusun wani tsohon diraktan banki kimanin N7bn
  7. Bata lokaci wajen daukan mataki kan jiragen ruwa biyu da hukumar Sojin ruwa ta kwace
  8. Fifita wasu jami’an EFCC kan wasu wadanda akafi sani da ‘Magu Boys’
  9. Kai wasu Alkalai kara wajen shugabanninsu ba tare da sanar da Antoni Janar ba
  10. Sayar da dukiyoyin sata ga yan’wansa, abokan arziki da abokan aiki.

 

Source:

Yusuf Salisu Buzu

Zuru Emirate New Media Reporters