Turnukun Dake Tsakanin Buhari Da Matar Data Dinga Zafgamar Ashariya A Landan-Bincike

Daga: Haji Shehu

Biyo bayan bincike da na gabatar akan Matar da ta zage shugaba Buhari ta uwa ta uba, bincike ya tabbatar da cewar Matar mai suna Saratu, Diyar marigayi Farfesa Ishaya Audu ce tsohon ministan harkokin waje a mulkin marigayi Shehu Shagari.

Yadda Saratu take zabga manyan ashariya kai ka san akwai wata kullalliya tsakanin ta da shugaba Buhari.

Bacin ran Saratu ga  Buhari ya sami asali ne tun lokacin da shugaba Buhari yayi wa gwamnatin Marigayi Shehu Shagari juyin mulki a jamhuriya ta farko, lamarin da ya kai ga tsare mahaifinta.

Bincike ya tabbatar da cewar korar mahaifinta aka yi daga aiki tare da tsare shi sakamakon juyin mulki, hakan tasa ya shafi karatun ta a birnin Landan, lamarin da ya kaita ga shaye-shayen muggan kwayoyi, ta daina zuwa makarantar ta har ta auri wani dan kasar Jamaica ( Rastafarian) kafun daga bisani auren su ya kare.

Mutane da dama sun bada shaidar cewa mahaifin Saratu, wato Farfesa Ishaya Audu mutumin kirkine, kuma ko kadan Saratu bata biyo kyawawan halayyar sa ba, don ko a lokacin mutane sunce siyasa ce da sha'anin mulki suka tsunduma shi cikin halin da ya tsinci kan shi.

Majiya @

https://www.facebook.com/208430435922061/posts/3876107542487647/?flite=scwspnss

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author