ULCER CIYO NE DA YA YAWAITA A CIKIN AL'UMMA

TAKAITATTUN BAYANAI AKAN CIWON OLSA.

 

----------------------

 

ME AKE NUFI DA CUTAR OLSA

 

OLSA (Ulcer) cuta ce da ke da yawa a cikin al'umma.

 

Olsa na nufin ciwo ko kurji da ke fitowa a cikin ciki ko hanji.

 

Idan an samu wannan kurji a cikin ciki (tumbin) ana kiran sa olsa na tumbi, idan kuma an samu a cikin hanji, ana kiran sa da olsa na hanji ko kuma duodenal olsa.

 

Da olsa na tumbi da na hanji duk suna da alamu kusan iri daya banbancin su baya da yawa.

 

ALAMOMIN OLSA

 

1. Ciwon ciki, musamman zafi a zuciya kamar ana hasa wuta. Ciwon na iya kasan cewa kafin cin abinci ko kuma bayan mutum ya ci abinci.

 

2. Jin wani abu yana tasowa daga cikin ciki ko kuma nauyin ciki, ma'ana mutum ya ji cikin sa yayi nauyi kuma babu daɗi.

 

3. Jin kamar mutum zai yi amai ko kuma taruwar yawu ko miyau a baki

 

4. Jin cewa mutum baya sha'awar cin abinci

 

5. Yin bayan gari gutsire gutsire kuma baƙi kotun

 

6. Aman jini

 

ABUBUWAN DA KE KAWO OLSA

 

1. Kwayar halitta mai suna Helicobacter pylori

 

2. Yawan shan maganin ciwon jiki ba bisa ka'ida ba.

 

3. Yawan shagalta da ayukka har ya kasance mutum baya cin abinci akan lokaci

 

4. Damuwa da yawan tunani

 

5. Abinci mai yaji ko maiko sosai

 

6. Yawan shan shayi ko coffee mara madara

 

HANYAR SAMUN WARAKA DAGA OLSA

 

Ana samun waraka daga olsa idan aka sha magani.

 

Ana kuma samun waraka idan aka guji ci ko shan abubuwan da ke kawo olsa, waɗanda muka ambata a sama.

 

Idan mutum ya sha maganin olsa kuma ya samu sauƙi, idan ya koma wa ci ko shan abubuwan da ke kawo olsa, to fa olsan N iya dawowa kuma sai an saka shan magani.

 

Ba a shan magani kala daya domin samun waraka. Ana bada magani kala biyu ko ukku ne kuma ana shan su sati daya ko sati biyu. Ya danganci tsananin olsan.

 

Wani olsa idan yayi yawa sai an bada allura na maganin olsa.

 

Allah Ya ƙara mana lafiya.

 

Allah Ya sa mu dace.

 

Asibiti A Tafin Hannun Ka

 

 

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author

I'am Muazu Muhammad from Gwandu Local Government Kebbi State