UWA ALJANNAR DUNIYA-MARYAM UMAR

"Sau da yawa wasu sukanyi wasarere da haƙƙoƙin iyayensu akansu, sukan manta da irin ɗawainiyar da suka ɗauka akansu kafin girmansu, sai bayan sun girma kuma kowa sai ya fara ƙyashin kyautatawa iyayen nasu"

-

"Dukkanin wanda ya rasa uwa a rayuwarsa, to haƙiƙa yayi babban rashi a rayuwarsa, domin takan yarda ta salwantar da komai nata domin taga ka inganta, dalilin hakane ya zamto cewa lallai babu mai ƙuntatawa iyayensa face sai asararre"

-

"Haƙiƙa uwa takan iya rainar ƴa'ƴa kimanin ashirin, koma fiyeda hakan, tun daga yarintar su har zuwa girmansu, amma su kuma bayan ta tsufa ta gajiya, sai da karo-karo sannan zasu ɗauki ɗawainiyarta, wannan shine galibin abinda yake faruwa ga wasu kenan, sun manta da irin wahalar da tasha akansu kafin girmansu, SubhanAllah, lallai uwa itace aljannar duniya, wanda ya rasa uwa yayi babban rashi a rayuwarsa, ya Allah ka saka wa iyayenmu da gidan aljannah, Ameen"

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author