Wallahi Ni Ba Mutanen Abduljabar ba, Ko Bayahude ne Ya Taho Guna Da Sunan Addini Zan Zauna Dashi-Sheikh Bello Yabo

Shahararren malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Muhammad Bello Yabo Sokoto, ya mayar da martani ga Malam Abduljabar Nasiru Kabara Kano.

Sheikh Bello Yabo yace koda Bayahude ne ya taho gurin sa da sunan addini to ya shirya zama dashi, ba mutanen Abduljabar ba.

Shehin malamin ya musanta zargin da ake yi masa na cewa, wani Dalibin Malam Abduljabar ya kure shi.

Sheikh Yabo yace, Sam wannan maganar bata da hujja domin a abin da nasan muyi Waya da Dalibin Abduljabar ta farko minti 13 da wani Abu, sai ta biyu inda Ni na kira shi mukayi awa daya da kusan minti daya wanda idan ka hada wayar da mukayi dashi takai kusan awa guda da mintuna 14.

"Amma sai suka yanke hirar suka dora ta mintuna 13 saboda ita suke kauna, wanda Ni nake ganin ba'a yimin adalci ba"inji sheikh Bello Yabo.

Da me bukatar wannan hirar zai iya magana ta WhatsApp akan wannan lambar 080330550199 ko kuma Ku ziyarci wannan Link din da ke kasa.

https://www.facebook.com/100284932021214/videos/275678307373594/

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author