September 18, 2020

Wani abun fashewa ya yi Ajalin wasu Mutane a Katsina.

Wani abun fashewa ya yi ajalin wasu mutane a katsina

photo credit: https://aminiya.dailytrust.com

Jaridar tace wani abu da ake zargin makami mai fashewa ne ya zama sanadin hallakar wasu mutane a kauyen Yammama da ke karamar hukumar mulki ta Malumfashi a Jihar Katsina”.

Abin ya fashe ne a daidai wurin da wasu manoma ke aiki a gona wanda nan take abin  ya yi sanadin wasu suka rasa rayuwarsu a wurin, wasu kuma suka samu raunuka.

“Na kirga gawarwaki shida bayan wasu biyar da aka kai asibiti, kuma jami’an tsaro sun killace wurin”, inji wani shaida, wanda yace mutanen da abin ya rutsa dasu masu neman nasawa baki ne wadanda ke aiki a gonar.

Kamar yadda jaridar ta bayyana cewar zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wani bayani game da adadin wadanda abin ya shafa a hukumance, haka kuma rundunar yan sandan jihar katsina ba ta kai ga yiwa yan jarida bayani ba.