Warware Matsaloli: Nazari Daga Makarantar Mufti Dr. Ahmad Abubakar Gummi

Nasan masu halarta da sauraron karatun addini a ƙasar Hausa sun saba da tsarin karantarwa da ya zama gama gari. Inda Malami ke buɗe littafi, yana jan baƙi da larabci yana fassara da Hausa yana sharhi.
Makarantar Dr Gumi ta bambanta da sauran makarantu, domin bayan tsarin karatu gama gari, Malam na shirya 'powerpoint presentations' a kan maudu'ai daban daban, ana 'demonstration', wani lokacin kuma ana ɗauko kalkuleta da 'tape' ko 'ruler' a tsunduma lissafi don ɗalibai su fahimci matsala da hanyar warware ta.
Bari mu leƙa aji muga yadda Malam ya warware wasu matsaloli ga ɗalibai.
1. Daga kilomita nawa ne matafiyi zai iya fara ƙasaru?
A mazhabar Imamu Maliku, ana fara ƙasaru ne a tafiyar da ta kai buruji huɗu wato kimanin Mil 48.
Shubuhar da aka riƙa samu a baya ita ce ta tunanin cewa Mil na Turawa daidai yake da Mil na Larabawa. Saboda haka da anyi 'converting' Mil 48 na Turawa zuwa kilomita, (Mil 1= kilomita1.609) sai lissafi ya tashi a 77.23 kilomita!
Amma ba haka lissafin yake ba! Mil na Turawa ba daidai yake da Mil na Larabawa ba!
In muka duba cikin littattafai, zamu ga cewa Mil na Larabawa daidai yake da zira'i 2000 a magana mashahuriya.
Zira'i kuma shine tsawon tazarar da ke tsakanin ɗan yatsa na tsakiyar hannun mutum matsakaici, zuwa guiwar hannun sa.
Daga nan sai Malam ya nemi ɗalibai uku masu matsakaicin tsawo su fito. Aka auna tsawon zira'in ko wannensu, aka samu kamar haka
Mutum na farko: 46cm
Mutum na biyu: 46cm
Mutum na uku: 52cm
Jimla = 144cm
Matsakaicin zira'i (Ave) = 48cm
Tunda matsakaicin zira'i ya kama 48cm, Mil ɗaya na Larabawa zai kama
48cm x 2000 = 96000cm = 960m
Daga nan Mil 48 na Larabawa zai kama 960 x 48 = 46080m = 46.08km
Kamar misalin kilomita 46 kenan.
An ƙididdige zira'in matsakaicin mutum a 50cm. In munyi amfani da 50x2000x48 = 4,800,000cm = 48 km. Saboda haka matafiyi zai iya fara ƙasaru ne in tafiyar ta kai kilomita 48, ba 77 da yan kai ba yadda aka ɗauka a baya.
2. Ya Ake Lissafin Nisabin Zakka da sauransu?
Na farko, a lissafo ƙimar Dinari guda
Dinari guda daidai yake da farashin giram 4.25 (4.25g) na gwal mai darajar karat 24
A ranar da akayi karatun (02/06/2017), giram ɗin gwal ɗin ya kama ₦17,500.
Saboda haka Dinari guda ya tashi a 4.25 x 17,500 = ₦74,375
A. Lissafin Nisabin Zakka:
Nisabin zakka shine Dinari ashirin wanda ya kama 20 x 74,375 = ₦1,487,500 kace miliyan daya da rabi
B. Ƙarancin sadaki
Ƙarancin sadaki shine rubu'in Dinari watau 1/4 x 74,375 = ₦18,593.75
C. Diyyar rai
Diyyar rai shine Dinari dubu watau 1000 x 74,375 = 74,375,000
Da zarar kasan farashin giram guda na gwal mai darajar karat 24, zaka iya yin lissafin nisabi a gida ba sai ka jira anyi lissafin a gaya maka ba.
Aliyu Ammani
U/Shanu Kaduna
01/04/20
Ƙarin bayani 1: na ɗauko maku waɗannan lissafin ne daga 'notes' ɗin da na ɗauka a karatun littafin Muwatta ranar 30/07/17; da Tafsirin Azumin Ramadan ranar 02/06/17.
Ƙarin bayani 2: zamanin da, ƙasashe da dama na amfani da Mil wajen lissafin tafiya. Amma awon ko wane Mil daban yake daga ƙasa zuwa ƙasa.
Ga wasu misalai, da ƙimar su a kilomita
Mil ɗin Sin (China) =0.5km
Mil ɗin Talmund na Isra'ila = 0.96 - 1.152km
Mil ɗin Rum = 1.852km
Mil ɗin Sikandinabiya = 10.0km
Credit: Dr. Aliyu Ammani Kaduna

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author