Ya Zama Dole Na Cika Burina Na Sake Zama Kungiya Daya da Messi - Neymar

Shahararren dan wasan  kungiyar kwallon kafa ta PSG Neymar ya bayyana aniyar ta sake buga wasanni tare da shahararren dan kwallon nan na Barcelona Lionel Messi a kungiya guda. 

Neymar wanda ya bayyana hakan, bayan da suka doke kungiyar kwallon kafa ta  Manchester United da ci 3-1 a gasar zakarun nahiyar Turai, wanda Neymar din ya ci biyu daga cikin su.

A yayin tattaunawar da manema labarai Neymar ya ce ya zama wajibi ya sake buga wasa tare da Messi a kungiya guda,  a kakar wasa mai zuwa.

Tun a shekarar 2017 Neymar ya bar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona zuwa kungiyar kwallon kafa ta PSG akan kudi mafi tsada a duniyar kwallon kafa ta nahiyar Turai  Euro na gugar Euro miliyan 222.

 

Kafin ya bar kungiyar Barcelona  Neymar da Messi da kuma Luis Suarez sun baiwa Barcelona babbar gudunmawa da kuma samun nasarorin a shekarun baya, sakamakon suna da masu karfin zura kwallon a raga, ga kuma  nasibin iya sarrafa kwallon dalla dalla.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author