Yadda Ake Hada WHITENING CREAM a Saukake

HANYOYIN SARRAFA SINADARAN KAYAN SHAFE-SHAFE DA TSAFTACE GIDA

 

SARATU MUHAMMAD SANI

 

08132534742

HAƘƘIN MALLAKA (M) Wannan littafi mallakar Saratu Muhammad Sani (Sarat M Sani) ne. A kula kada a juya wannan littafin ta kowace hanya ba tare da izinin marubuciya ba.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

SHEKARAR BUGA LITTAFI © 2017

 

AN SAKE BUGAWA 2020

 

 

GABATARWA

Sana'a rayuwar matasa. Babu shakka sana'a itace rayuwar matasa, saboda sai kanada abinyi kakejin komai yana tafiya maka yadda kakeso, kakejin rayuwar ka fes fes bakajin damuwa na wayyo kai Allah yau Kana son lalurar naira 100 amma bakada yadda zakayi.

Babu shakka ita sana'ar hannu ba ƙaramar muhimmiyar abu bace, musamman ga al'umma ko ince musamman garemu mata, saboda tana iya zamowa:

v Sanadin wadata.

v Samun yanci ga kai da kuma ƙasa baki ɗaya.

v walwala.

v Hana ta'addanci (misali sata, yaudara da sauransu)

v Da kuma hana zaman banza tare da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Da dai sauran taimakon da Sana'a keyima al'umma.

Ganin irin wannan yasa nayi tunanin bada tawa gudumuwwa ga rayuwar matasa yan'uwa na, saboda irin muhimmanci, da rawar da matasa ke takawa ga rayuwar al'umma.  Sai nake ganin babu abinda yafi cancanta ga matashi musamman ma matashiya mace irin ya zamana tanada wani abun dogaro dakai ko  tana aikin gwamnati ko batayi, idan ma tana aiki riƙe wani bangare na sana'a ba ƙaramin taimakawa yake cikin rayuwa ba to bale wacce bata aiki kusan ita wajibun gareta ma ta nemi sana'ar yi.

Inajin kamar nayi kuka idan naga yadda yan matan mu suke zubar da ƙimarsu ga samari, duk akan kuɗin da bai taka kara ya karya ba. Ko kuma kaga uwa mace ta zubar da ƙimarta ga saurayin yar'ta ko makamancin haka, ko kuma yau ki gansu wannan gida da sunan roƙo gobe wancan.

Idan ina tafiya naga matashi majiyi ƙarfi yana jira mai kudin unguwarsu ya fito ya samu abinda ya bashi, ko kuma naganshi an kama da sunan yayi sata, ko kuma naganshi cikin mashaya, zuciyata tana ɗaci da ƙuna, duk da ni ba wata mai ƙarfi bace amma inajin wannan damuwa inama. ......" ire iren wannan su ka jefani rubutu, dan ganin na bada tawa gudummuwa ga matasa ko dan mu gudu tare mu tsira tare, ta hanyar dogaro ga kai.

Abin tambaya anan da ya kamata matasa muyima kanmumusamman mata, wai menene aibu kina mace matashiya kin koyi sana'ar ɗinki kinzo kina ƙoƙarin ƙirƙiro styles masu kyau yanda zaki ja ra'ayin costumers naki ? ina laifi idan kika koyi saƙa( knitting) kina ƙoƙarin fitadda sababbin patterns da sauran salo salo na kwalliyar saƙa, yadda shima zaki ja ra'ayin costumers naki? Ashe ci bayane dan kina mace kinzo kin koyi kaloli daban daban na yadda zaki hada kayaki na cosmetics, shima kinzo products ɗinki kin tsaya sosai kina packaging nasu yadda zasu sami shiga wurare da dama ba tare da an raina aikin ki ba? Wa zai zageki dan kin ƙoƙarta kin koyi yadda ake kitso, ko saloon suma ko yaushe kina ƙirƙiro abinda zai jawo miki ƙarin customers? kai ko gyaɗa kike ƙullawa a leda cikin gida ana zuwa saye ko aya, Popcorn, kai ga ƙananin sana'oi nan daban daban da ban lissafa su ba,  saboda yawan rubutu da zaki fara dasu wanda kece da kanki zaki sarrafasu ki maidasu wata babbar sana'a ta azo a gani. Yafi miki kina yawon gidajen dangi maula, ko gidajen ƙawaye, da aron kaya, ko dogaro ga samari, da Alhazawan da kike tarawa saboda kawai su ɗauke miki buƙatunki na yau da kullum. A ƙarshe ki dawo nadama bayan kin zubar da ƙimarki da darajar iyayenki kin kuma cutar da ya'yan ki da zasu zo idan kinada rabon samun ya'yan.

Haka kaima matashi namiji, akwai sana'oi kala daban daban da zaka zaɓa ka riƙa yi sannu a hankali har ta zamo maka babbar sana'a. Sai nake ganin yafi maka maula, da yawon dangi, da kuma zaman banza, daƙyar da suɗin goshi da roƙo da komai, kake samun na sayen wata shadda ko yadi,  tashi tsaye ka nemi abinyi yafi maula. Ya kamata mu farka da ga baccin da muke tin lokaci bai ƙure mana ba.

Haƙuri da jajircewa ga komai shi ke kawo nasara.

Wannan littafi mai suna HANYOYIN SARRAFA SINADARAN KAYAN SHAFE-SHAFE DA TSAFTACE GIDA

Ya ƙunshi kalololin mayuka (Creams/lotion) sabulai (soap), cleansers, turaruka  na gyaran jiki, face powder(hoda ta fuska), da sauran abubuwa masu muhimmanci dake cikin wannan littafi  kala daban daban har guda  68. Wanda mace ko namiji zai haɗa yana gida ba sai ya wahala zuwa wani wuri koyo ba, insha Allah cikin sauƙi indai anbi wannan littafin daki-daki baza'aji wahalar haɗa kayakin ba. 

 

Sarat M. Sani

 

WHITENING CREAM.

Kayan hadin da ake bukata:

v Shea butter

v Allatoin

v Carrot oil

v Coconut oil

v Beeswax

v Stearic acid

v Glycerin

v Saffron ( a drop)

v Apricot oil

v Vit b3

v Licorice

v Kojic power

v Arbutine

v Glutathione

v Mulberry extract powder

v Giga

v Emulsifying wax.

v Aha (cokali 1)

v Kala ( Color)

v Preservative/germal plus, citric acid

v Madarar turare me ƙamshi

v Mazubi

YADDA ZA'A HAƊA

A zuba ruwa ba me yawaba a roba me kyau, sai a kawo kojic powder, mulberry extract powder, da dai sauran chemicals da suke gari ne a zuba cikin ruwan a narka su, daban daban a ajiye su gefe, sai a narka Shea butter,  beeswax, emulsifying wax da kuma coconut oil, kada a cika wuta, Kaɗan za'asa wutar har ya narke , sai a sauke. A motsashi aɗan ajeshi gefe yaɗan rage zafi, sai a kawo wannan ruwan powders din da aka jika daban daban a zuba ciki ana zubawa ana motsashi, Sannan a zuba carrot oil Shima a motsashi sosai, Sannan a zuba apricot oil, glycerin, vitb3, saffron,da sauran kayakin dana lissafa a sama. Daga ƙarshe sai a zuba kala  da akeso, sannan a zuba turare da preservative a motsashi sosai ya haɗe, shikenan sai a zuba a mazubi

A rika kula sosai idan ana aiki da chemicals, a guji abinda zaisa su taɓa jiki.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author

GLOBNG HUB - Best for All Globng Hub and SGL is for interested content creators who wants to share their experience to the whole world, you can create account with us, when your account is approve you can then proceed to create contents ranging from entertainment, sports, politics, health and fitness, society news, technology, business and industrial, lifestyle, education, pet and animals etc. The interested thing is you will get paid as far as your contents/articles worth paying. To Register click on the link below https://globng.com/register