September 24, 2020

Yadda Kishiyoyi suka daure Dan Abokiyar Zamansu a turken Awaki na tsawon shekaru two

Kamar yadda wani sako ke ta yawo a kafafen sadarwa na WhatsApp da Facebook an gano wasu iyaye da suka daure yaronsu na tsawon shekaru two ba tare da bashi abinci ba, ga yadda labarin yake


“Kamar yadda labari yazo mana Wannan yaron da kuke gani Sunanshi Jibril Aliyu kuma yana Unguwar Badariya Area dake cikin garin Birnin Kebbi, a jihar kebbi.

Labari ya samemu cewar kishiyoyin Mahaifiyar shi ce suka daureshi cikin turken Tumakai na tsawon Shekaru Biyu tun bayan rasuwar Mahaifiyar shi.

Kuma bai samu kulawa na bashi abuncin ci, sai dai yaci abuncin dabbobi da kashin shi ma’ana tutunshi sune abunda yake ci, inda yanzu haka jami’an tsaro suka kama kishiyoyin Mahaifiyar shi da suka daure hadi da mahaifinshi inda suka garzaya da zuwa (Police Station)

Kuma bayanai sun tabbatar da cewar an garzaya da yaron zuwa Asibitin Sir Yahaya Memorial Hospital dake birnin kebbi don bashi agajin gaggawa

Allah ya bashi lafiya, kuma ya shirya mata masu irin wannan hali Amin.”

Daga Real sani Twoeffect Yawuri

Leave a Reply