Yadda Na Bankawa Surukata Ciki: In Ji Wani Matashi

Daga Wakilin Mu

Wani matashi daya bukaci a boye sunan sa ya bayyana yadda wani ibtila'i ya faru da shi da kuma irin halin da yake ciki a yanzu, cewar Matashin yayin da yake magana a cikin shahararren shirin nan na Talk Show in Radio, ya ce a baya shedan ya rinjaye shi inda ya kwanta da mahaifiyar matarsa har ta kai ga an haifa wa matar tashi kani.
 
Ya ce a yanzu haka hankalin ya tashi kuma a rude yake cikin wannan yanayi.
"Lokacin da na hadu da matata, komai na tafiya daidai, muna soyayya ba kama hannun yaro.""Amma an ce kumatun da zai sha mari baya jin bari, Soyayyar mu ta yi nisa har ta kai ga budurwar tawa ta gabatar da ni gaban iyayenta, amma abin mamaki shine yadda na ga mahaifiyarta kamar ba ita ba, saboda irin Kirar da Allah Ya yi mata"
 
"Ta haifi matar tawa ce sa'ilin tana shekara 15, abubuwa na ta gudana har ta kai ga tana ziyarta ta lokaci-lokaci, kafin auren mu da matar tawa wacce yarta ce" abin da ya fara da ziyara ne, wani lokaci muna zaune da mai gida na sai ga ta nan ita da wasu kawayen ta biyu a wani wurin cun abinci, har ta gabatar musu da ni"
 
Matashin ya kara da cewa bayan da ta siya mishi kayan goge wuya ne dai a wannan ranar, shedan ya gitta bayan da direban ta ya makara zuwa dauko ta, har ta kai sun kwanta, kwanciyar da ta haifar ga zuwan kani ga matata.
 
@majiya
Dimokuradiyya

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author