'Yan Sanda Sun Kashe Dan Bindiga Daya Da Samun Bindugu Biyu A Hannunsa A Katsina

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Rundunar 'yan sanda ta jihar Katsina, karkashin jagorancin kwamishinan'yan sanda Sanusi Buba sun yi nasarar kashe wani dan bindiga har lahira da samun bindiga kirar Ak47 a hannun sa a cikin garin Danmusa a jihar Katsina.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar SP Gambo Isa ya sanar da manema labarai a ranar Laraba 17 ga watan Feb, 2021.
SP Gambo Isa ya bayyana cewa, da misalin karfe biyu na daren ranar Talata, yan bindigar dauke da bindigogi kirar Ak47, sun je fashi gidan Alhaji Sani Bello dake cikin garin Danmusa, da niyyar su yi mashi fashi da makami. Baturen dan sanda na karamar hukumar ya samu labari, nan take ya ja ragamar jami'an tsaro, inda suka je wajen su ka yi musayar wuta, bayan samun nasara sun kashe daya daga cikin barayin.
 
Inda har mu ka samu bindiga kirar Ak47 da harsashi guda goma sha hudu, Ana ci gaba da binciken wurin da aka yi wannan fafatawa da su, saboda da yawa daga cikin su sun samu raunuka ko mun kashe wadansu daga cikin su. Ana kan bincike.
A wani labarin kuma, duk dai a daren na ranar Talata, inda baturen yan sanda na karamar hukumar Kankara da jami'an yan sandar shi, sun fita suntiri akan hanyar Zango zuwa Fawwa, su ka yi kicibus da wasu 'yan bindiga, a ka yi musayar wuta, barayin nan su ka ji tsoro suka ruga. Mun samu bindiga kirar Ak49 a hannun su da madaukan harsashe guda biyu watau (Magazines) da kuma harsashai guda biyar. Wannan bindigu suna hannun mu ana kan binciken.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author