Yan sanda sun Kashe yan fashi 2 da Mace 1 sun kama tarin makamai a jihar Ebonyi

Hukumar yan sandan a jihar Ebonyi ta kashe wasu mutane biyu da mace guda daga cikin gungun Yan ta'addan da makami da suka kai hari wani Banki a Onueke ranar Talata.

E0ZtXdkXIAEnLKU.png


Jami'in hulda da rundunar yan sandan Najeriya Mista Frank Nba ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar ga manema labarai.

Ya bayyana cewa yan sanda sun kashe mutum biyu tare da wata mace guda da ke tare da su yayin musanyar wuta da bindigogi. Sakamakon haka yan sanda sun kama bindigogi guda 2 kirar AK47 da albarussai masu yawa

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author