YANZU-YANZU | An Saka Ranar Bikin Naɗin Sarautar Sarkin Dawaki Babba A Masarautar Kano

Alhaji Aminu Babba Dan Agundi wanda shine tsohon Sarkin Dawaki Mai Tuta, wanda ya rasa rawaninsa tun zamanin Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero kimanin shekaru da suka shuɗe, yanzu haka ya na shirin samun nasarar sake dawowa Sarauta wadda tuni Masarautar Kano ta nemi sahalewar gwamnatin Kano don aiwatar da naɗin.
 
Sai dai duk da ƙoƙarin da ya daɗe ya na yi wajen ganin Kotu ta dawo masa da Sarautarsa ta Sarkin Dawakai Mai Tuta, da Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya rabashi da ita sai dai hakan yaci tura, bayan shafe kwanaki da rashin nasararsa a Babbar Kotun Ƙoli ta Najeriya, Masarautar Kano ta sanar da bashi sabuwar Sarauta mai suna Sarkin Dawaki Babba wadda shine karo na farko da za’a fara yinta a jihar.
 
Wannan Sarauta ta Sarkin Dawaki Babba tana daga cikin Sarautu waɗanda masu rike da ita a jihar zasu dinga zaɓar Sarkin Kano a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso, kuma wannan Sarauta ahlin gidan Sarkin Dawaki Mai Tuta Babba Dan'agundi ne zasu dinga yin wannan Sarauta ta Sarkin Dawaki Babba kamar yadda yake a sabuwar dokar Masarautu ta Shekarar 2020.
 
Sai dai tun bayan sanarwar baiwa tsohon Sarkin Dawaki Mai Tuta Hakimin Gabasawa Aminu Babba Sarautar, cikin watan Yulin Shekarar 2020 wannan batu yake kaikawo a bakunan jama’a, wanda kuma sai a wannan lokaci ne majiyarmu ke samun labarin cewa ana gabda nada Sarkin Dawaki Babba wannan Sarauta da ake sanya ran za’a gudanar bayan Sallah.
 
Yanzu haka dai ansanya ranar 28 ga watan Mayun Shekarar nan ta 2021 da muke ciki domin Naɗa Alhaji Aminu Babba Dan'agundi a matsayin sabon Sarkin Dawaki Babba, kuma Danmajalisar Sarki a Kano kamar yadda wasu majiyoyi da suka nemi a sakaya sunansu suka rabbatarwa da majiyar mu.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author