Yanzu-Yanzu: Burutai da sauran Tsofaffin Hafsoshin Tsaron Nigeria sun dira a Majalisa

 

Yanzu-Yanzu: Burutai da sauran Tsofaffin Hafsoshin Tsaron Nigeria sun dira a Majalisa

 

Tsofaffin Hafsoshin tsaron Nigeria da shugaba Muhammadu Buhari ya zaba a matsayin sabbin jakadu sun dira majalisar dattawa don tantance su da tabbatar da su, Vanguard ta ruwaito.

Mambobin Majalisar sun fara tantance su sai dai an hana ‘yan Jarida shiga. Tsoffin hafsoshin tsaron sun dira Majalisar ne da misalin karfe 11:32 na safiyar Alhamis, 18 ga Faburairu, 2021. Sun hada da Abayomi Olonisakin, Tukur Buratai, Ibok-Ete Ekwe Ibas, da Sadique Abubakar.

Isar su ke da wuya su ka shiga ofishin mai baiwa Buhari shawara kan majalisar dattawa, Sanata Babajide Omoworare, wanda ya shigar da su dakin taro. Dai-dai misalin karfe 12, shugaban kwamitin, Adamu Muhammad Bulkachuwa, ya bukaci su sanya labule da mambobin kwamitin.

Ana shiga irin wannan labule ne domin tattauna yadda za'a yi saboda gudun samun sabani gaban jama'a.

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata, 9 ga Faburairu, 2021, ya bukaci majalisar dattawa ta tarayya da ta tabbatar da tsoffin hafsoshin tsaron Najeriya matsayin Jakadu zuwa kasashen waje. Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar shugaba Buhari a zauren majalisa ranar Talata.

Source: Legit Hausa

 

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author

GLOBNG HUB - Best for All Globng Hub and SGL is for interested content creators who wants to share their experience to the whole world, you can create account with us, when your account is approve you can then proceed to create contents ranging from entertainment, sports, politics, health and fitness, society news, technology, business and industrial, lifestyle, education, pet and animals etc. The interested thing is you will get paid as far as your contents/articles worth paying. To Register click on the link below https://globng.com/register