Wata babbar kotun tarayya dake Abuja, ta bayar da umarnin tsare Sanata Ali Ndume a gidan gyaran hali dae Kuje, sakamakon kasa kawo Abdulrasheed Maina gaban kutun bayan karɓar belinsa da yayi.
Tun a baya ne dai Sanata Ndume ya tsayawa Maina wanda ake zargi da handime maƙudan kuɗaɗe na hukumar fansho, inda Ndume ya karɓi belinsa.
Sai dai tun bayan da kotun da bayar da belin nasa, har zuwa wannan lokaci Maina bai ƙara bayyana a gaban kotun ba.
You must be logged in to post a comment.