YANZU-YANZU: Tsohon Shugaban Kasa, Jonathan Ya Ziyarci Jihar Bauchi

Daga: Lawal Muazu Bauchi

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dira a filin jirgin sama na Abubakar Tafawa Balewa dake jihar Bauchi a yau Talata domin ziyarar kaddamar da ayyuka na kwana daya.
 
Tsohon shugaban kasan ya samu tarba daga Gwamna Bala Mohammed, mataimakin sa Sanata Bala Tela, Sakataren Gwamnati, Sabi'u Muhammad Baba, shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, Dakta Ladan Salihu, shugaban jam'iyyar PDP na jihar Bauchi, Alhaji Hamza Koshe Akuyam da dubban magoya baya da mukarraban gwamnati.
 
Tsohon shugaban kasan ya ziyarci jihar Bauchi ne domin kaddamar da wasu ayyukan tituna da gwamnatin tsohon ministansa na Abuja ya shimfida a fadin jiahr Bauchi.
 

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author