Yanzu-Yanzu Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 13 Tare Da Sace Shanu 500 A Jihar Kebbi

A karamar hukumar Danko-Wasagu da ke jihar 'yan Bindiga sun kai wani farmaki inda suka kashe mutane 13 tare da sace shanu kimanin 500 a ranar Alhamis 8 ga watan, Aprilun 2021.

Bayan wani farmaki na ranar  Laraba 7 ga watan, Aprilun 2021 inda yayi sanadiyyar kashe jami'an tsaro guda 7 tare da fararen hula 7.

Majiyar mu ta sami cewa da misalin karfe 4 na ranar Alhamis ne Yan bindigan da suka fito ta yankin Malekachi a karamar hukumar Mariga ta jihar Niger da ke makwabtaka da jihar Kebbi, inda suka shigo ta Bakin ruwa sai suka yi dirar mikiya a garin Ayu daga nan kuma suka shiga wani kauye da ke yankin kasar Kanya, nan da nan sukai tayin harbi, sannan suka kora garken shanu sama da 500 a kauyukan da ke tsakanin Ayu da Kanya.
 
Majiyar tamu ta cigaba da samin bayanai na cewa Yan bindigan sun kashe mutane 13 a harin sannan suka yi satar shanu tsakanin garuruwan Ayu,  Muzaba, Matseri, Dutsen Kuma, da sauran garuruwa da ke makwabtaka da yankunan.
 

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author