Yawanci Musulmai Wayayyu Ne Amma Pantami Baya Cikinsu, Inji Obadiah Mai Lafiya

Tsohon Mataimakin Gwamnan babban bankin Najeriya, Obadiah Mailafiya ya bayyana cewa, Yawanci Musulmai wayayyu ne, Sai dai yace amma irin su Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Ali Pantami wanda a Salaf ne dake bin Ibn Taymiyya suna da matsala. Yace aƙidarsu irin ta su Hitler ce da Nazi wadda idan baka tare dasu basu ɗauke ka a matsayin mutum ba. Yace a ƙarkashin irin koyarwarsu ne aka samu kungiyoyin Alqaeda, Al-Shabab da ISWAP.
 
Mai Lafiya ya kuma ƙara da cewa, babbar matsalar irin su Pantami masu haddar Qur’ani shine suna ɗauko abinda aka rubuta shi da Larabci suce zasu fassara zuwa Hausa ko turanci wanda hakan abune mai matukar wahala.
 
Ya bayyana haka ne a hirar da aka yi dashi a jaridar Tribune da aka tattauna dashi.
Mai Lafiya yace Pantami na nuna alamar son komawa Madina, yace suna maraba da hakan dan kuwa basa buƙatar irin shi a Najeriya. Yace Pantami ya kawowa Najeriya wani tsari waishi na NIN kuma ana ta shigo da Fulani daga kasashen waje ana musu rijistar wannan NIN ɗin dan ace sune suka fi yawa.
 
Yace akwai shirin Jihadi ne da ake yi a Arewa.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author