Za A Aiwatar Da Dokar Sanya Takunkumi A Kano Ba-sani-ba-sabo – Baffa Dan Agundi

Daga Abdullahi Muhammad Sheka

Shugaban hukumar karota a jihar Kano, kuma shugaban kwamitin karta kwana na tabbatar da dokar sanya takunkumin rufe baki don hana wanzuwar cutar korona a kano, Hon Baffa Babba Dan Agundi ya sha alkawarin tabbatar da dokar babu sani ba sabo.

Hon Baffa Babba dan Agundi wanda shi ne shugaban karota da kuma hukumar kula da ingagancin masu siyan kayan amfani yace, wajibi ne ayi ta'ammali da takunmi rufe bakin kamar yadda aka ba da umarni.

Da yake zantawa da 'yan jaridu Hon Dan Agundi yace akwai yiwuwar a rufe kasuwannin Jihar Kano saboda yadda yan kasuwar ke nuna halin ko in kula da dokar da akasa inda Janzakaran kamar yadda ake masa kirari ke shan alkawarin cewa wajibi ne abi dokar ko a fuskanci fushin hukuma.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author