Zuba Kuɗaɗe A Masana’antar Kanywood Sadaka Ce Mai Gudana Da Za'a Amfana Anan Duniya Da Gobe Ƙiyama-Momo

Fitaccen jarimin masana’antar Kanywood Aminu Shariff Momo ya ce, a yanayin da ake ciki yanzu da a gina Masallatai da Islamiyyu gwara a zuba kuɗaɗen a harkar shirya fina-finan Hausa.
Momo ya bayyana hakan ne cikin shirn ‘Barka Da Hantsi’ na gidan rediyo Freedom da safiyar Laraba.
Momo ya kuma yi kira ga mawadata da su dinga tallafawa masana’antar ta Kannywood da kuɗaɗe kamar yadda suke tallafawa marayu da sauran masu buƙata ta musamman.
Momo ya ce al’umma za su iya zabar irin fina-finan da suke so ayi musu da suka shafi al’ada da dabi’un Malam Bahaushe matuƙar za su dinga bada tallafin kuɗaɗe ga masana’antar.
"Kuma ya kamata a ringa fitar da kuɗaɗe daga cikin tsarin zakka da za a ringa shirya fina-finan Hausa da sauran shirye-shirye domin jama’a su amfana." Inji Momo

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author